14 Maris 2022 - 17:49
Wani Dan Wasan “Lantanis” na kasar Masar Ya yi Wa Duniya Tuni Akan Halin Da Al’ummar Palasdinu Ke Ciki Na Tsawon Shekaru 74

Dan wasan na kasar Masar mai suna Ali Faraj, ya ce; Shekaru 74 kenan al’ummar Palasdinu suna cikin wahala a karkashin mamayar HKI

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dan wasan na kasar Masar wanda ya lashe wata gasa a birnin London na Birtaniya ya yi jawabi a gaban dubban masu sha’awar wasan cewa, yana da cewa yin wannan maganar zai iya jawo masa matsala,amma kuma wannan shi ne gaskiya da hakikanin abinda yake faruwa a kasa, kuma yanzu ana cakuda tsakanin wasanni da siyasa”

Faraj ya cigaba da cewa; Taso da wannan batu ba abu ne wanda kasashen yammacin duniya suke son ji ba, sannan ya kara da cewa: “ A wannan lokacin dukkanin duniya tana tausayawa al’ummar Ukireniya saboda yakarsu da kasar Rasha take yi, don haka ya zama wajibi mu yi tuni da cewa, Palasdinawa ma suna cikin wahala.

342/